Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Hallaka Wasu 'Yan Boko Haram Guda 15


Sojojin Operation Lafiya Dole

Rundunar sojin Najeriya ta Operation lafiya dole ta bada sanarwar kashe wasu 'ya'yan kungiyar Boko Haram guda 15 a wani farmaki da ta kai kan 'yan kungiyar Boko Haram din a yankin tafkin Chadi.

Sanarwar dake dauke da sa hannun mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole, Kanal Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa an samu wannan nasarar ne da hadin gwiwar jami'an soji da kuma na kasar Kamaru a kudancin yankin tafkin Chadi inda suka kai hari kuma suka tarwatsa tungar 'yan kungiyar a kokarin da suke yi na kawo karshen ragowar 'yan kungiyar din a wannan yankin a bayan kauyukan da ke Arewacin Borno.

Rundunar sun fatattaki 'yan kungiyar a maboyarsu bayan musayar wuta da suka ringa yi da maharan har suka hallaka maharan guda 11 a kauyen Gomaran da ke yankin tafkin chadi.

A wani harin da suka kai wasu wuraren guda biyu, sun fatattaki wasu 'yan kungiyar a yankin Birgi da Maula a karamar hukumar Bama da Dikwa da ke jihar Borno inda suka hallaka wasu 4.

Rundunar ta samu damar gano wasu makamai wanda suka kunshi bindigogi masu daukar harsashi daya irin na maharba. da bindigar toka guda, da karamar bindigar hannu, da babura 4, da injinan ban ruwa 6, da na wuta guda 2.

Haka kuma rundunar ta cafke wadansu yan kungiyar guda biyu da ransu sanye da kayan sarkin soja da ake kira Camouflage .

Ha'ila yau sanarwar ta kara da cewa rundunar ta samu fito da wasu mutane 4 da mata 33 da kuma kananan yara 16 daga maboyar 'yan ta'addan da aka yi garkuwa da su. A halin yanzu kuma ana tantancesu don a mika su inda ya kamata.

Saurari rahoton Haruna Dauda Biu

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:51 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG