Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Mayu 17, 2018: Tashin Hankali A Tsakanin Iyali, Kashi Na Daya


Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu

A lokutan baya, duk lokacin da aka ambaci cin zarafi a tsakanin ma’aurata akan danganta shi ne da cin zarafin mata, da danne hakkokinsu da kuma kuntata masu ta hanyoyi dabam dabam.

Sai dai aka wayi gari, aka shiga samun yanayi inda lamarin ya sauya aka shiga samun mata ba kawai suna cin zarafin mazansu ba, amma ake yawan samun mata suna kashe ‘ya’yan abokan zamansu da kuma mazan da suke aure da suka hada da na baya bayan nan da wata mace ‘yar shekaru goma sha shida ta kashe mijinta mai shekaru talatin da biyu da haihuwa a birnin Kano.

Ta haka shirin Domin Iyali ya gayyaci masu ruwa da tsaki domin neman sanin abinda yake janyo haka da kuma matakan da za a iya dauka na shawo kan wannan matsala.

Saurari cikakken shirin.

Tashin Hankali tsakanin Iyali:10:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:29 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG