Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunkurin Hambarar Da Gwamnatin Burundi


Shugaban Kasar Burundi, Pierre Nkurunziza

Wani Janar a kasar Burundi ya ce ya hambarar da gwamnatin shugaba Pierre Nkurunziza, wanda ya fice a kasar domin halartar taron koli na kungiyar kasashen yankin, inda za a tattauna game da rikicin siyasar kasar.

Janar Godefroid Niyombare, ya gayawa kafofin yada labarai masu zaman kansu cewa zai kafa wani kwamiti da zai maido da zaman lafiya da hadin kai a kasar. Wakilin Muryar Amurka, Gabe Joselow, wanda ke Bujumbura babban birnin kasar, yace mutane suna ta nuna farin cikinsu bayan wannan sanarwar.

Sai dai ya ce babu tabbacin ko Janar din na da cikakken goyon bayan sauran sojin kasar. Wakilin na Muryar Amurka ya kuma ruwaito ce sojojin sun yiwa gidan radiyon kasar kawanya, sannan an ji harbin bindiga a birnin, yayin da ‘yan sanda suke artabu da masu zanga zanga.

Masu adawa da burin na shugaban sun ce hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, yayin da masu mara mai baya suke fadin akasin hakan, saboda a cewarsu, ‘yan majalisu ne suka zabe shi a daya daga cikin wa’adin da ya yi, ba masu kada kuri’a ba.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG