Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Hana 'Yan Saudiyya 18 Shiga Turai Akan Kisan Jamal Khashoggi


Yarima Mohammed bin Salman
Yarima Mohammed bin Salman

Akalla kasashen Turai 26 suka haramtawa 'yan Saudi Arebiya mutum 18 da ake zargin su da hannu wajan kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi, wanda ya ke wa jaridar Washington Post aiki.

A yau Litinin ministan harkokin wajen kasar Jamus ya fada cewa, gwamnatin Jamus za ta hana wasu 'yan kasar Saudiyya su 18, shiga yankin nan na Schengen wato wasu rukunin kasashen tarayyar Turai 26, wanda ba sai da fasfot ake shigarsu ba, saboda ana zargin su da alaka da kisan gillar da aka yi wa dan jaridar kasar Saudiya Jamal Khashoggi.

Ministan harakokin wajen, Heiok Maas ya ce sai da ya tuntubi kasashen Faransa da Birtaniya kafin ya fito da wannan dokar.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce an yi masa cikakken bayani akan faifan rediyon da aka nada yayin da ake kashe dan jaridar nan a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya, dake Santanbul a watan da ya gabata.

Aamma ya ce bashi da niyyar ya saurari kaset din saboda tashin hankalin da yake cikinsa.

Shugaba Trump ya fada a ranar Asabar cewa a ranar Talata mai zuwa, gwamnatin Amurka zata bada cikakken bayanin abun da ta gano na kisan da aka yiwa Khashoggi a ranar 2 ga watan Oktoba da ta gabata.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG