Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbe Wani a Amurka Yayin Zanga-zangar Kisar Jacob Blake


Lokacin da 'yan sanda suka harbe mutumin
Lokacin da 'yan sanda suka harbe mutumin

An harbe wani mutum har lahira yayin da aka shiga dare na uku a jere na zanga-zanga a garin Kenosha da ke jihar Wisconsin, saboda harbe wani Baƙar fata da 'yan sanda suka yi ranar Lahadi.

Wanda aka kashe din yana daya daga cikin mutane da dama wadanda aka ji wa raunuka da harbi yayin zanga-zangar daren jiya Talata zuwa safiyar yau Laraba.

Kafafan yada labarai sun ce harbin ya faru ne a yayin wata arangama tsakanin masu zanga-zangar da wasu da ke tsaye kusa da wani kotu da ke cikin gari, inda masu zanga-zangar suka yi ta fada da ‘yan sanda na sa’o’i da dama har sai da aka fitar da su daga yankin.

Zanga-xangar adawa da kashe Jacob Blake
Zanga-xangar adawa da kashe Jacob Blake

Bidiyo na wayar salula aka saka a kafofin sada zumunta, sun nuna wani mutum yana harbe-harben kan taron bayan da ya fadi a kasa.

Zanga-zangar ta ranar jiya Talata ta zo sa'o'i bayan mahaifin Jacob Blake, mai shekaru 29, baƙar fata wanda aka harba ranar Lahadin, ya ce ɗansa ya samu nakasa daga kugunsa zuwa kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG