Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbi Sowore A Wajen Zanga-Zanga


Omoyele Sowore a ranar 24 ga watan Disambar 2019.
Omoyele Sowore a ranar 24 ga watan Disambar 2019.

Bayanai sun yi nuni da cewa an harbe shi ne a cinyarsa ta dama, lamarin da ya ji masa rauni, kuma rahotanni na nuni da cewa an garzaya da shi asibiti domin a yi masa magani.

Rahotanni daga Abuja, babban birnin Najeriya na cewa an harbi mai fafutkar kare hakkibn bil adama Omoleye Sowore da bindigar da ke cilla hayaki mai sa kwalla.

Bayanai sun yi nuni da cewa an harbe shi ne a cinyarsa ta dama, lamarin da ya ji masa rauni, kuma rahotanni na nuni da cewa an garzaya da shi asibiti domin a yi masa magani.

“Yanzu wata ‘yar sanda mai suna ACP Atine ta harbe ni a dandalin Unity Fountain da ke Abuja, kada a sassauta fafutukar ko da sun kashe ni.” Sowore ya rubuta a shafinsa na Twitter dauke da hoton raunin da aka ji masa.

Sowore shi ke jagorantar gangamin samar da sauyi a Najeriya, inda hukumomi ke zarginsa da tunzura mutane don a sauya gwamnati.

Karin bayani akan: Sowore, Unity Fountain, ACP, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

An dai sha kama shi a wuraren zanga-zanga a baya. Lokaci na baya-bayan da aka sako shi shi ne a watan Janairun bana.

Jami’ai sun cafke shi ne a wajen wata zanga-zangar nuna adawa ga gwamnati da aka yi a ranar jajiberin sabuwar shekara.

Sowore ya taba tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben 2019 da Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe.

XS
SM
MD
LG