Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Jefe Wata Mace a Pakistan


Mata suke kuka kan gawar Farzana Iqbal, wacce danginta suka kashe saboda ta auri wani da take so.

Cikin wadanda suka kai mata hari harda mahaifinta da 'yan uwanta a gaban wata kotu a birnin Lahore.

An jefe wata mace mai juna biyu har lahira a Pakistan a harabar wata kotun kasar, saboda ta auri mutuminda take so ba tareda amincewar danginta ba.

Matar mai suna Farzana Parveen ‘yar shekaru 25 da haifuwa, ta auri Mohammed Iqbal, cikin ‘yan watanni da suka wuce ba tareda yardar iyayenta ba.

‘Yansanda suka ce kusan mutane ashirin ‘yan danginta ciki harda mahaifinta da ‘yan uwanta suka lakada mata duka da sanduna da duwatsu da idon rana jiya talata, mutane suka taru suna kallo a harabar wata kotu dake birnin Lahore.

Lauyanta yace mahainfin Farzana ya shigar da kara gaban kotu yana zargin mijin ‘yarsan ta sace masa ‘ya, su kuma suna kan hanyar zuwa kotu domin su kalubalanci karar ne suka far mata.

Iqbal ya gayawa manema labarai cewa matarsa tana da cikin wata uku.
XS
SM
MD
LG