Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yi Bikin Tunawa Da Makomar Bakar Fata A Burtaniya


Gidan aje kayan tarihin bauta na kasa da kasa.
Gidan aje kayan tarihin bauta na kasa da kasa.

A kasar Burtaniya an yi bikin tunawa da rayuwar Bakar fata a Burtaniya na shekara shekara. Wannan karan an mai da hankali ne kan rawar da Burtaniya ta taka game da bauta.

An yi bukin Watan Tarihin Bakar Fata a Burtaniya. A garuruwa da biranen Burtaniya musamman ma masu kunshe da Bakaken fata da dama irinsu London da Liverpool da Manchester da dai sauransu, kungiyoyi da hukumomi sun shirya bukukuwa iri iri.

Wakilinmu a London Sani Dauda ya ce saidai kuma a yayin da ake shirye shiryen wasan kwaikwayo da muhawarori kan makomar Bakar fata a Burtaniya, wani sashin kuma na korafi ne da cewa batun rayuwar Bakar fata a Burtaniya ba ta sake zani ba.
Bukukuwan da bana sun mai da hankali ne kan matsayin Burtaniya game da cinikin bayi da mulkin mallaka.

Esther Stanford Xosei ta kungiyar neman diyya daga Burtaniya kan laifukan cinikin bayi da mulkin mallaka ta ce “A dunkule dai biyan diyya na nuna gyara da yin sulhu da kuma maido da mutuncin al’ummar da tarihi ya nuna an gallaza masu ta wajen nuna rashin imani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG