Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dokar Hana Fita Baki Daya a Maiduguri


Sojoji su na farautar 'yan bindigar Boko Haram da suka kai farmaki kan filin jirgin saman Maiduguri da wani sansanin mayakan sama dake kusa da nan cikin daren da ya shige.

Hukumomi sun kafa dokar hana fita waje baki daya a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, a bayan da wasu tsageran da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka kai farmaki.

‘Yan jarida a garin na Maiduguri sun ce an kai harin na asubahin yau litinin a babban filin jirgin saman Maiduguri da kuma wasu sassan dake wurin, cikinsu har da sansanin mayakan saman Najeriya dake wannan filin jirgi.

Sojoji sun rufe dukkan hanyoyin motar zuwa filin jirgin a bayan wannan farmaki. Wani jami’in gwamnatin Jihar Borno ya fadawa VOA cewa sojoji su na binciken ko an bar wasu nakiyoyi a wurin, sannan su na farautar ‘yan bindigar da suka kai harin.

Rundunar sojojin Najeriya ta fada a cikin wata sanarwa cewa ta samu nasarar fatattakar wani yunkurin da ‘yan Boko Haram suka yi na shiga cikin wasu sassan garin Maiduguri, kuma ta yi barna mai yawa a kan tsageran.

Ta ce kura ta lafa yanzu haka a kewayen filin jirgin saman da kuma kauyen Jantilo dake nan.

Har ila yau, rundunar sojojin ta Najeriya ta yi kira ga jama’ar Maiduguri da su mutunta wannan dokar hana fita waje baki daya, yayin da sojoji da jiragen yaki suke farautar ‘yan ta’addar da suka kai harin.

Wannan shi ne karon farko da aka kafa dokar hana fita dare da rana a garin Maiduguri tun 2009.

Jihar Borno tana daya daga cikin jihohi uku na yankin arewa maso gabashin Najeriya inda shugaba Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci a watan Mayu, a wani yunkurin murkushe kungiyar Boko Haram.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG