Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dokar Ta Baci A Kasar Turkiyya


Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ayyana dokar ta ‘baci biyo bayan kokarin juyin mulkin da bai samu nasara ba na ranar juma’a, wanda ya girgiza shi da gwamnatinsa.

Turkiyya zata kasance cikin dokar ta baci har tsawon watanni uku, Erdowan ya bayyana haka ne ta gidan talabijin a daren jiya Laraba, bayan nan ne kuma ya fara wata ganawa jami’an tsaron kasar da kuma ministocinsa.

Erdowan yace dalilin kafa dokar ta bacin shine domin “a dauki matakan da suka kamata wajen dawo da dimokaradiyya da doka da oda.” Shugabannin Turkiyya dai sunce sojoji ba zasu karbi ikon kasar ba a tsawon lokacin da za a ‘dauka.

A daren jiya Laraba ne ‘daruruwan masu goyon bayan Erdogan su ka cika dandalin Taksim dake Istanbul da sauran gurare a fadin Turkiyya domin nuna goyon bayansu ga shugaban kasar su da kuma kare sake faruwar kokarin juyin mulki da shugaban yace zai iya ‘kara faruwa.

An dai nuna jawabin shugabanne ta ‘katon majigi da aka saka a dandalin Taksim, jama’ar dake kallo lokacin da aka bayyana dokar ta ‘bacin sun barke da Shewa.

XS
SM
MD
LG