An gano cewa ‘yan Boko Haram na shigar da makamai cikin Najeriya daga ruwan tafkin chadi, hakan yasa gwamnatin tarayya ta umarci sojojin ruwa da su bude runduna a gurin, a cewar daraktan labarai a hedikwatar sojojin ruwan Najeriya, Kaftin Sulaiman Dahun.
Baya ga tafkin Chadi, rundunar sojan ruwan ta kuma kakkafa ‘karin wasu rundunonin a sauran sassan Najeriya. Haka kuma rundunar ta yi tunanin bude sabbin rundunoni a duk inda ake da babban kogi a fadin kasar.
Masanin tsaro Saleh Jingir mai ritaya, ya ce kafa runduna da sojojin ruwa su kayi a yankin tafkin Chadi wani abu ne mai matukar muhimmanci, ganin yadda ake amfani da ruwan wajen shigar da makamai.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum