Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Sabuwar Kungiyar ‘Yan Kasuwa Da Sarrafa Albasa a Najeriya


Duba da irin alfanun da albasa ke da shi a jikin bil'adama da kuma irin tashin gwauron zabi da farashinta ya yi a Najeriya, wanda ba a taba gannin irinsa ba a tsawon lokaci ya sa aka kafa sabuwar kungiyar ‘yan kasuwa ta masu sarrafa albasa ta kasa.

An kafa wannan kungiya ne don mayar da hankali wajen bunkasa noma da sarrafa albasa ta hanyar samar da kudaden shiga ta fannin tattalin arzikin Najeriya.

A shekarar 2020 ne al’ummar Najeriya suka koka a kan yadda kayakin masarufi da sauran albarkatun noma suka yi tashin gwauron zabi, babu kamar na albasa da kusan a kowanne girki ake amfani da ita.

Matsalar dai ta kai ga sai gidan wane-da-wane ake amfani da albasa wajen girka abinci, kuma ana gani rikice-rikicen da ake yi a kasar da kuma ambaliyar ruwa su suka taka gagarumar rawa ga tsadarta.

Aliyu Maitasa Isa, sabon shugaban kungiyar ‘yan kasuwa da masu sarrafa albasa ta kasa baki daya, ya ce kungiyar za ta hada manoman albasa da ‘yan kasuwa da masu sarrafata wuri daya, kuma hakan zai kawo babban ci gaba ga manoma da ‘yan kasuwa da kasar baki daya.

Isa Muhammad manomi ne daga jihar Gombe, ya bayyana farin cikinsa na kafa wannan sabuwar kungiya ya na mai cewa burinsa shi ne a samu iri mai kyau na albasa, da takin zamani, da kayayyakin noma.

Wani babban kalubale da manoma ke fuskanta shi ne rashin samun tallafi duk kuwa da kokarin da gwamnati ke yi wajen maida hankali ga harkokin noma a kasar, kamar yadda Alhaji Isa Adamu manomin albasa daga jihar Adamawa ya bayyana.

A bangaren gwamanti kuwa, babban sakataren ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dakta Nasiru sani Gwarzo, ya ce babban tallafin da gwamnati za ta bai wa manoma shi ne kawo musu tsarin kasuwanci na zamani da kuma tallafi karkashin bankin Industry wanda zai taimaka a ba manoma da ‘yan kasuwa bashi.

Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00


Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG