Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayanin Buhari Ga Majalisa Na Iya Amfanar ‘Yan Bindiga – Minista Malami


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

A daidai lokacin da Majalisar Wakilan Najeriya ke jiran bayyanar shugaban kasa gabanta yau Alhamis, domin amsa tambayoyi game da halin tabarbarewar tsaro da kasa ke ciki, Ministan Shari’a ya ce bayanin Buhari ga Majalisa na iya amfanar ‘yan bindiga

Ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ya ce ganin damar shugaban kasa ne ya bayyana gaban Majalisa don amsa tambayoyi kan lamuran tsaro.

Malami na magana ne kan amsa gayyatar Majalisar Wakilai da Shugaba Buhari ya yi, don yin bayani kan tabarbarewar tsaro da kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamiala, ya ba da tabbacin amsa gayyatar bayan ganawarsa da Shugaban a fadar Aso Rock.

Kazalika, mai taimakawa shugaban kan labarun yanar gizo Luretta Onochie, ta ba da tabbacin Shugaban zai bayyana gaban hadaddiyar Majalisar Dokokin a yau Alhamis.

Malami ya ce lamuran tsaro da boye bayanan sirri duk suna hannun Shugaban kasa, don haka ba ikon Majalisa ba ne ta gayyace shi ya yi bayani a bainar jama'a kan lamuran tsaro.

Don haka Malami ya ce ganin damar Shugaban ne ya amsa gayyatar ko kuwa ya ki amsawa. Kuma yaki dan zamba ne. Don haka sa Shugaban kasa ya bayyana matakansa gaban Majalisa ba zai zama da alheri ba ganin makiya na iya samun bayanan.

Saurari tattaunawar Umar Farouk Musa da Ministan Shari’ar Najeriya, Abubakar Malami.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00


Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG