Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Tarihi: Trump Da Kim Jong Un Sun Hadu


Shugaba Trump da Kim Jong Un a lokacinda sukea hadu a Singapour.
Shugaba Trump da Kim Jong Un a lokacinda sukea hadu a Singapour.

An kafa wani babban tarihi a kasar Singapore, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya hadu da shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong Un domin yin taron koli da aka tsara. Trump, shi ne shugaban Amurka na farko da ke kan mulki da ya hadu da shugaban Korea ta Arewa a tarihin huldar diplomasiyyar kasashen biyu.

A karon farko kuma a wani mataki na kafa tarihi, shugaban Amurka Donald Trump da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa Kim Jong Un sun hadu.

Shugabannin biyu sun hadu ne da safiyar yau Talata (lokacin Singapore), inda suka gaisa a gaban totocin kasashen biyu da aka jera a bayansu.

Daga baya kuma sun shiga cikin otel din da taron ke gudana, inda suka fara tattaunawa kan batun da ake tsammanin na kwance damarar makaman nukiliyan Korea ta Arewa ne.

Amma gabanin hakan, shugaba Trump da Kim, sun dan zauna na wani lokaci domin ganawa da manema labarai.

“Lallai ba abu mai sauki ba ne zuwa nan.” Inji Shugaba Kim.

Ya kara da cewa, “zamanin da ya shude ya haifar mana da kalubale kan yadda za a samar da maslaha, amma kuma mun yi hobbasa mun tsallake duk wani shinge, yanzu kuma ga mu a nan yau.”

Shi kuwa shugaban Amurka ya jaddada abin da Kim ya fada ne yana mai cewa, “wannan gaskiya ne.”

Trump ya kara da cewa, “lallai za mu cimma gagarumar nasara, kuma wannan abin alfahari ne, kuma ba na wata tantama, za mu kulla kyakkyawar dangantaka.”

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce a daren ranar Talata shugaba Trump zai bar kasar ta Singapore.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG