Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Wata Sabuwar Kungiyar 'Yan Tawaye a Sudan Ta Kudu


Sojojin Sudan ta Kudu
Sojojin Sudan ta Kudu

Wani babban kwamandan sojin Sudan Ta Kudu, wanda ya balle a watan jiya, ya ce shi ma yanzu ya kafa tasa kungiyar 'yan tawayen don yakar Shugaba Salva Kiir.

Janar Thomas Cirillo Swaka ya fitar da wata takardar bayani jiya Litini, wadda a ciki ya shelanta da kansa a matsayin Chairman kuma Babban Kwamandan kungiyar national Salvation Front.

Nan take dai ba a san karfin wannan kungiyar ba, ko idan za ta hade da kungiyar Sudan People's Liberation Army, kungiyar 'yan tawayen da ta shafe shekaru uku ta na fafatawa da gwamnatin Kiir.

Shirin Muryar Amurka na Turanci mai suna South Sudan in Focus ya samu kofin bayanin na Cirillo, wanda ya zargi gwamnatin Kiir da kwace iko da dukiyoyi don kawai amfanar 'yan kabilarsa ta Dinka, kuma ta yadda ake kwarar sauran kabilun da su ma su ka taka rawa wajen wajen kwato 'yanci daga Sudan.

Wasu sassan bayanan kuma sun zargi gwamnatin Kiir din da almundahana, da kasa samar da abuwan bukata ga jama'a da kuma yin watsi da bangaren noma, wanda shi ne batu na karshe cikin manyan batutuwan da ake takaddama akansu a wannan kasar, inda tsananin fari ya jefa miliyoyin mutane cikin rashin abinci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG