Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Farmaki A Birnin Hodeida Mai Tashar Jirgin Ruwa A Yemen


Jiragen Yaki a Yemen
Jiragen Yaki a Yemen

Rundunar hadin gwiwa karkashin jagoranci Saudi Arabia mai goyon bayan gwamnatin Yemen, a yau Laraba ta kaddamar da farmaki a kan muhimmin birnin Hoodeida mai tashar jirgin ruwa.

Kungiyar tawayen Houthi ita ce ke rike birnin Hodeida da kuma babban birnin Yemen Sana'a. Hadaddiyar daular larabawa da take cikin rundunar hadin gwiwar, ta fada yau Laraba cewa, yau ne wa'adin da aka baiwa yan tawayen Houthi su bar birnin mai tashar jirgin ruwa ke cika.

Hodeida birnin ne mai muhimmanci wurin shiga da kayan abinci da sauran kayayyakin taimako. Kafin fara wannan yakin shekaru uku tsakanin 'yan tawayen Houthi da gwamnatin shugaba Abdu Rabu Mansour Hadi, kasar ta yi fama da rashin abinci, kana Majalisar Dinkin Duniya ma tace akwai mutane sama da miliyan 20 a yanzu dake bukatar taimako.

Yakin ya sha hana shiga da kayayyakin taimako, yayin da kuma gwamnatin kasar mai neman mafaka ta fitar da wata sanarwa a yau Laraba cewa, sake kwato Hodeida wata gagarumar nasara ce a wannan yaki ta sake karbar ikon kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa, sama da mutane dubu goma aka kashe, galibi kuma ta farmaki ta sama da rundunar hadin gwiwar ke yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG