Accessibility links

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a kauyukan karamar hukumar Langtan ta Kudu a jihar Pilato

Wasu 'yan bindiga sun farma kauyuka a karamar hukumar Langtang ta Kudu suka kashe mutane 28. A gumurzun da ya biyo baya tsakanin dakarun tsaro da maharan an sake kashe mutane 20 lamarin da ya sa adadadin mutanen da suka mutu ya haura zuwa 48.

Yayin da yake kara haske game da lamarin kakakin rundunar a jihar Pilato Kaften Salisu Mustafa ya ce ranar ashirin da takwas da daddare suka samu labarin cewa wasu sun kai hari a wasu kauyukan da suka hada da Magama. Ya ce da suka tura dakarunsu zuwa wuraren sai 'yan bindigar suka bude masu wuta lamarin da ya yi sanadiyar kashe mutane ashirin. Ya kara da cewa sun kama wasu daga cikin maharan har da baburan da suka yi anfani da su.

Wasu cikin maharan sun gudu amma sai da suka cinna ma gidajen muaatne wuta. Kakakin sojojin ya tabbatar da cewa sun soma yiwa wadanda suka kama tambayoyi.

Kawo lokacin rahoton nan kura ta lafa an kuma jibge dakaun tsaro da dama. Ana harsashen cewa harin nada nasaba da abun da ya faru makon da ya wuce inda aka kashe shanu da suka ci anfanin gona da aka shuka.

Yanzu dai an tsaurara matakan tsaro a duk fadin jihar Pilato domin shirin ko ta kwana

Zainab Babaji nada karin bayani.
XS
SM
MD
LG