Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Ce Tilas Ta Rage Wasu Hukumomin


Wata unguwa a Abuja, babban birnin Najeriya kuma cibiyar gwamnati

Gwamnatin ta ce tilas a sake duba tsarin dukkan ma'aikatu da hukumomi domin hade masu aiki iri guda da kawar da wadanda ba su tabuka komai.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ba zata iya gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, kuma ta hanyar da ta fi dacewa tare da yin amfani ga jama'a ba, sai fa idan ta sake nazarin dukkan ma'aikatu da hukumomin da take da su domin hade wadanda suke gudanar da aiki iri guda, da kawar da wadanda ba su tabuka wani abu ga ci gaban al'umma da kasa.

Gwamnatin ta bayyana wannan matsayin ne a bayan da ta amince da rahoton Kwamitin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Mr. Steve Orosanya, wanda ya duba yadda za a sake fasalin ma'aikatu da hukumomin gwamnatin Najeriya.

Sai dai kuma, tuni 'yan kwadago a Najeriya suka yi kashedi game da korar ma'aikata da zata iya faruwa idan har gwamnati ta aiwatar da shawarwarin kwamitin da ya tanadi rushe daruruwan hukumomi, ko hade su.

Ministan yada labaran Najeriya, Mr. Labaran Maku, ya fadawa wakilin Muryar Amurka, Umar Faruk Musa, cewa ai ba a kai matsayin da za a iya sanin yadda wannan aiki zai shafi ragewa ko korar ma'aikata ba tukuna.

Labaran Maku ya kara yana cewa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG