Accessibility links

An Kai Hari A Karamar Hukumar Karen Lamurde, Jihar Taraba

  • Grace Alheri Abdu

Mutane suka hallara a wurin da aka kai harin kunar bakin wake a jalingo, a jihar Taraba.

Wadansu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a wani banki da kuma caji ofis din 'yan sanda a karamar hukumar karen Lamido ta jihar Taraba.

Wadansu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan fashi ne sun kai hari a banki da kuma ofishin gunduma na ‘yan sanda a karamar hukumar Karen Lamido a jihar Taraba a daren jiya. A cikin hirarsu da wakilinmu Abdulwahab Mohammed ta wayar tarho wani dan jarida jarida dake aiki da jaridar Sunrise ta jihar Taraba ya bayyana cewa, mutane sun kauracewa garin domin fargaban bacin rana.
XS
SM
MD
LG