Accessibility links

An Kai Hari Kan Wani Masallaci a Kasar Kuwaiti


'Yansanda sun killace Masallacin da aka kaiwa hari a kasar Kuwaiti

A halin yanzu kuma…Kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kai harin kunar bakin waken da ya kashe akalla mutane 10 a wani masallaci da ke babban birnin kasar Kuwaiti.

Wata kungiya da mai alaka da mayakan na IS mai suna Najd Province, ta ce ita ta kai harin.

Dan kunar bakin-waken ya ta da bam din ne, yayin da dimbin mutane suka taru a masallacin domin gudanar da sallar Juma'a.

Har ila yau Kungiyar ta Najd Province, ta ce ita ke da alhakin kai wasu hare-hare makamantan wannan a wasu masallatan 'yan Shi'a biyu da ke Saudi Arabia a 'yan makwannin nan.

XS
SM
MD
LG