Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kare Hakkin Bil Adam Ta Ja Kunnuwan Kasashen Turai Akan Bakin Haure


Bakin Haure akan tekun Baharum da aka ceto

Kungiyar kare hakkin bil Adam ta kira kasashen turai da su shirya su amsa tambayoyi akan yadda suke ceto hakin haure dake yin anfani da tekun Baharum zuwa gudun hijira

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasa da kasa Human Rights Watch, ta yi kira ga kungiyar tarayyar Turai “da ta ci gaba da shirin aikin ceto” na ‘yan gudun hijirar da ke neman mafaka wanda hakan ya kai su ga tsalla kogin Baharum, yayinda Turai take fadi tashin tsara shiri sahihi na tunkarar wannan matsala.

Kungiyar tafitar da wani rahoto da yake kira ga shugabannin kungiyar tarayyar Turai da su gaggauta ‘daukar mataki a lokacin da zasu fuskanci tambaya kan ‘yan gudun hijira a taron kolin da za’a gudanar sati mai zuwa wato 25 da 26 ga watan Yuni.

Kungiyar tace tayi hira da kimanin mutane 150 wadanda suka isa kasar Italiya da tsibirin Greek, wadannan guraren biyu dai sune inda masu gudun hijirar suka fi zuwa daga Gabas ta Tsakiya da Afirka. Yawancin mutanen sunce cin zarafin bil Adam ne babban dalilin da yasa suke gujewa kasashen su.

A kwai yawan karuwar shiga cikin hatsari a lokacin da ‘yan gudun hijirar ke kokarin tsallaka tekun. Masu kula da lamuran sunce yanayin ya kazanta ne musamman a Libiya, sai kuma arewacin Afirka inda yawancin masu gudun hijirar ke fitowa. Mafi yawancin ‘yan gudun hijirar suna fitowa ne daga Siriya da Najeriya da Mali da kuma Eritiriya inda mutane ke kokarin gujewa yaki.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG