Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari Ma Salman Rushdie A New York


SALMAN RUSHDIE
SALMAN RUSHDIE

Marubuci Salman Rushdie ya sake tsallake rijiya da baya yau Jumma'a a birnin New York bayan da wani mutum ya yi yinkurin hallaka shi.

Salman Rushdie, marubucin nan wanda wani rubutu da ya yi ya janyo masa barazanar hukuncin kisa daga Iran a shekarun 1980, yau Jumma'a wani mutum ya kai masa hari a wani dandalin taro yayin da yake shirin gabatar da lacca a yammacin New York, kuma da alamar maharin ya caka masa wuka a wuya.

Wani dan jaridan kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya shaidi yadda wani mutum da ya tinkari Rushdie a kan mumbarin a cibiyar Chautauqua, ya shiga naushinsa ko daba masa wuka sau 10 zuwa 15 yayin da ake gabatar da shi. An tura marubucin mai shekaru 75 ya fadi a kasa, kuma an kama mutumin.

Ana jinyar gaggawa ma Rushdie bayan taba masa wuka
Ana jinyar gaggawa ma Rushdie bayan taba masa wuka

Musulmi da dama na daukar Littafinsa na 1988 mai suna "Ayoyin Shaidan" a matsayin sabo. Zanga-zangar adawa da rubutun na Rushdie mai yawan gaske ta barke a duniya, ciki har da tarzomar da ta kai ga mutuwar mutane 12 a Mumbai.

Nan ana rugawa da Rushdie asibiti bayan daba masa wuka da maharin ya yi
Nan ana rugawa da Rushdie asibiti bayan daba masa wuka da maharin ya yi

An haramta littafin a Iran, inda marigayi Ayatollah Ruhollah Khomeini ya ba da fatawa, ko kuma doka a 1989, yana kira da a kashe Rushdie.

XS
SM
MD
LG