Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Harin Kunar Bakin Wake a Jihar Borno


Ma'aikatan Lafiya
Ma'aikatan Lafiya

Anyi asarar rayukka da dama a wani mummunan harin da aka kai a wani sashen na jihar Bornon Nigeria.

Wani dan kunar bakin wake ya kai hari a wani masallaci a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya a jiya Laraba kuma ya kashe akalla mutane goma.

Wadanda suka shedi al’amarin sun ce maharin ya shiga masallacin ne dake garin Gamboru, jim kadan kafin sallar asuba inda ya tada bam din, masallaci ta rushe ta koma buraguzai.

Yazuwa dai yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin, amma yana da alamar hare haren Boko Haram, kungiyar da ta kwashe tsawon shekaru takwas tana tabka ta’addanci da zub da jinni da zummar kafa daular musulunci a arewacin Najeriya, lamarin da ya kai ga asaran rayukkan mutane dubu ashirin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG