Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kaiwa wata makaranta hari a jihar Delta


Motoci ne ke konewa a harabar Cocin Saint Theresa, a sakamakon irin hare haren da aka kai.

'Yan sanda a kudanci Nigeria, sunce wasu mahara sun jefa bam cikin wata Makarantar Arabiya a jihar Delta harma mutum 7 sunji rauni.

'Yan sanda a kudancin Nigeria sunce wasu mahara sun jefa bam cikin wata makarantar Arabiya a kudancin kasar harma suka raunana mutum bakwai. Wannan al'amari ya faru ne bayan hare haren da aka kai coci coci a wasu sassan kasar.

Hukumomi sunce jiya Talata da dare wannan al'amari ya faru a jihar delta lokacinda aka jefawa makarantar bam daga wata mota. Yara shidda suna daga cikin wadanda suka jikatta.

Wannan harin ya biyo bayan hare haren da aka kai ranar Lahadi ana bikin Kirisimeti da suka kashe akalla mutane talatin da shidda.

Kungiyar Boko Haram tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai hare haren na ranar Kirisimeti. Wasu Kiristoci a arewacin Nigeria sunyi kashedin cewa karin tarzoma suna iya hadasa rikicin addini a kasar.

Bayan ganawar da yayi da shugaba Jonathan a jjiya Talata, sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar na uku yace babu rikici tsakanin Musulmi da Kirista maimakon haka, yace fada ne tsakanin bata gari da mutanen kirki.

Aika Sharhinka

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG