Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kakkabo Jirage A Gumurzun Isira'ila Da Siriya


Tarkacen jirgin yakin Isira'ila
Tarkacen jirgin yakin Isira'ila

Ana can ana musayar wuta tsakanin kasar Isira'ila da Siriya mai samun goyon bayan Iran. Wannan ya biyo bayan harbe wani jirgi mara matuki da aka cillo shi daga Siriya zuwa Isira'ila wanda Isira'ila ta kakkabo ta kuma ce na Iran ne. Da Isira'ila ta kai harin da ta kira na ramuwar gayya kuma sai aka harbo jirgin yakinta

Kafar labaran gwamnatin Siriya, yau dinnan Asabar, ta ce kasar Siriya na kan mai da martani kan abin da ta kira “wata sabuwar takala ta Isira’ila,” bayan wani harin da Isira’ila ta kai a tsakiyar kasar.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Tsaron Isira’ila Jonathan Conricus ya saka wani sako a kafar twitter mai cewa Kasar Isira’ila na kan, abin da ya kira, “luguden wuta kan wasu muradun Siriyar da kuma kasar Iran wajen 12 da ke cikin kasar ta Siriya, a matsayin martanin takalar Isira’ilar da Iran ta yi”

Gidan Talabijin din Siriya ya ce ana iya jin karar barin wutar da ake kan yi har a lardin Reef Dimascus, wanda ke daura da babban birnin kasar.

Tun da farko Isira’ila ta ce ta kakkabo wani jirgin Iran mara matuki, wanda aka cillo shi daga kasar Siriya bayan da ya shiga kasar Isira’ila da daren jiya Jumma’a.

A gumurzun da aka yi a yau dinnan Asabar, sojojin Siriya sun kakkabo wani jirgin yakin Isira’ila samfurin jet ta wajen amfani da makamin harbo jirgi.

Ma’aikatar Tsaron Isira’ila ta ce matuka jirgin sun diro daga jirgin ta amfani da laimar dira to amma daya daga cikinsu ya samu munanan raunuka.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG