Jami'an hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka sun kama baki dake zama kasar ba bisa ka’ida ba kusan su 700 a wani samame da su ka kai kan wasu masana’antun sarrafa abinci a jihar Mississippi jiya Laraba, wannan shine kame mafi girma da aka taba yi a Amurka a cikin shekaru 10.
An sanya mutanen da ake kyautata zaton bakin haure ne a cikin wata motar bas a wajen masana’antun a garuruwa shida dake jihar Mississippi, a yayin da ‘yan uwa da abokai suka zura ido suna kallon ikon Allah. Wasu daga cikin su sun yi ta fadi “ku kyale su” da karfi, a lokacin da motar bas din ke kwashe bakin.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce wasu daga cikin bakin sun yi kokarin tserewa amma aka kama su.
Jami'an hukumar shigi-da-fici da kuma kwastam ta Amurka sun ce an kai bakin hauren wani barikin soja don gudanar da bincike akansu. Wasun su ma an makala masu wata na’urar lantarki a kafa don a sa ido akan su, a yayinda suke jiran ranar da zasu je kotu.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum