Accessibility links

An Kama Hanyar Zaman Lafiya A Najeriya-Solomon Dalong

  • Grace Alheri Abdu

Wadansu mutane suna bude baki

Lauya mai zaman kanshi Solomon Dalong yace ziyara da Kirista suke kaiwa gidajen Musulmi domin bude baki tare alama ce ta zaman lafiya a Najeriya.

Wata kungiyar hadin kan Musulmi da Kirista a arewacin Najeriya ta kaiwa Sheikh Dahiru Bauchi ziyara a gidanshi dake garin Kaduna.

Kungiyar ta kai ziyarar ne karkashin jagorancin lauya mai zaman kanshi Solomon Dalong da nufin kara karfafa dankon zumunci tsakanin Kirista da Musulmi da kuma yarda da juna.

Da yake hira da manema labarai yayin ziyarar, Solomon Dalong ya bayyana cewa, bude baki da ake yi tsakanin mabiya addinan biyu a garuruwa dabam dabam na kasar alama ce cewa, an fara samun zaman lafiya, ya kuma yi kira da a ci gaba da daukar matakan cudanya da fahimtar juna.

XS
SM
MD
LG