Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Masu Zanga-zangar Lumana Sama Da 50 a Iran


Da babbar murya ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi Allah wa dai da kama masu zanga-zangar lumana da aka yi a kasar Iran, kamar yadda rahotannin dake fitowa ke cewa cikin kwanaki biyu an kama mutane sama da 50 dake zanga-zanga cikin biranen Iran kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

A jiya Juma’a ne ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da wata sanarwa dake cewa, “rahotanni masu yawa na nuna yadda ‘yan Iran ke gudanar da zanga-zangar lumana a fadin kasar.”

Ta ci gaba da cewa “shugabannin Iran sun mayar da kasa mai yalwar tattalin arziki da al’adu zuwa kasa mai fama da matsalar tattalin arziki. Wadanda ke daukar matakai na ban takaici dake kawo tashin hankali da zub jini da kuma hargitsi.”

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kira ga dukkan kasashen duniya, da su fito su nuna goyon bayansu ga mutanen Iran da kuma bukatunsu na neman ‘yanci da kawo karshen cin hanci da rashawa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG