Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Kashe Dumbin Mutane A Mumbai


Wuraren ncin abincin da wutar ta shafa
Wuraren ncin abincin da wutar ta shafa

Wata gobara da ta kama a wani dogon gini dake Mumbai a kasar Indiya tayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

A kalla mutane 15 ne suka rasu da yawa kuma suka jikata bayan da wata gobarar da ta tashi a wani babban gini da ke babban birnin hada-hadar kudade na India Mumbai. Akasarin wadanda suka rasa rayukansu mata ne.


Wutar ta fara ne daga wani wurin cin abinci da ke can saman ginin kimanin karfe 1 na dare daga bisani kuma ta kama ginin baki daya.


Shugaban kasar Indiya, Ram Nath Kovind ya yi amfani da shafin sa na twitter inda ya mika sakon gaisuwar sa ga iyalai da 'yan uwan wadanda abin ya shafa ya kuma yi musu fatan Allah ya kara sauki. Motocin 'yan kwana kwana 8 ne sukayi aiki na fiye da awa 5 kafin suka kashe wutar , ana ci gaba da binciken abinda ya haddasa gobarar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG