Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Matan da Ake Zaton Su Suka Kashe Kim Jong Nam


Kim Jong Nam yayan shugaban Kriya ta Arewa wanda aka kashe a Malaysia a hannun hagu

Da taimakon naurar daukan hoto dake filin saukar jiragen sama na kasa da kasa a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia, 'yan sandan kasar suka matan da ake zargin suna da hanu a kisan dan uwan shugaban Korea ta Arewa.

A yau Alhamis, 'yan sanda a Malasiya,sun ce sun kama mace ta biyu dangane da kashe Kim Jong Nam, wanda dan'uwan ne ga shugaba Kim Jong Un.

Hukumomi sun bayyana matar a matsayin Siti Aisha, 'yar shekaru 25 da haihuwa, wadda su ka ce ta na da fasfo din kasar Indonesiya, kuma daga hotunan da nu'arar daukan hoto ta dauka a filin jigrin sama taka samu nasarar cafke ta..

Kamun na ta ya biyo bayan kamun wata matar kuma da aka yi a filin Jirgin saman kasa da kasa na Kuala Lumpur a Malasiya.

'Yan sanda sun bayyana ta da Doan Thi Huong, wacce ke tafe da takardun izinin tafiya na kasar Vietname.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG