Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wan Shugaban Koriya Ta Arewa A Malaysia


Kim Jung Nam wan shugaban Kariya ta Arewa
Kim Jung Nam wan shugaban Kariya ta Arewa

An kashe yayan shugaban Koriya ta Arewa Kim Jon Un, mai suna Kim Jong Nam ranar Litinin, a wata tashar jirgin sama a Malaysia, kamar yadda wani jami'in 'Yansanda na kasar yayi bayani.

Jami'in 'Yansandan kasar Fadzil Ahmat, yace Kim Jong Nam ya fadi da rashin lafiya a tashar jirgin sama ta kasa da kasa dake Kuala Lumpur, bayan yace yaji kamar "wani ya kama ko ya rufe masa fuska ta bayansa." Wacce ake zargin mace ce, wacce take dauke da wani mayani da aka jika da guba.

Da farko an kai shi dakin shan magani ko Clinic dake asibitin, amma suka yanke shawarar su kai shi babban asibiti, amma rai yayi halains a hanya.

Kim Jung Nam daga hagu da kaninsa Kim Jung Un shugaban Koriya ta Arewa daga dama
Kim Jung Nam daga hagu da kaninsa Kim Jung Un shugaban Koriya ta Arewa daga dama

Rahotanni da aka samu tunda farko, sun ce wasu mata 'yan leken asiri daga Koriya ta Arewa suka soki Kim Jon Nam da allurai da aka dura da guba, suka tsere cikin wata motar Taxi.

Baturen 'Yansandan yace zuwa yanzu basu kama kowa ba kan wannan lamari.

Kim Jon Nam ya bata da kaninsa shugaban Koriya ta Arewa, tun lokacin yake zaman gudun hijira galibi a wani yankin Macau dake karkashin China.

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG