Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kama Salah Abdeslam da ake nema mame da harin Faransa


Babban Wanda Ake Zargi a Harin Birnin Faris Na Watan Nuwabar Shekarar 2015, Salah Abdeslam

An cafke wani kokuwar wanda ake tuhumar da kitsa kai harin birnin Paris a ranar 13 ga watan Nuwamba shekarar data gabata, inda aka damke shi a kasar Belgium, kamar yadda ministan kasar ya bayyana.

‘Yan sanda ne suka cafke Salah Abdeslam a wani samamen da suka kai jiya Juma’a a wata unguwa mai suna Molenbeek da ke birnin Brussels. Mahukunta sun ce Salah ya ji rauni a kafa inda yanzu haka yake kwance a asibiti.

Ministan shige-da-fice na Belgium Theo Francken ya tabbatar da wannan labara har a shafinsa na Twitter inda rubuta cewa, “Mun Kama Shi”. Gigan talbijin ya nuna yadda ‘yan sandan suke tasa keyar mutumin cikin motarsu bayan kama shi.

Wani Kakakin gwamnatin kasar yace har da wani Monir Ahmed Alaaj da ake kira Amine Choukri aka jiwa rauni, shima aka mika asibiti. Kafin dai cafke wadannan ‘yan ta’addar sai da jami’ai suna gano tambarin yatsunsu a rukunin wasu gidaje a wata unguwa da suka kai samame makon da ya gabata.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG