Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wani Akwati Da Na'urar Kera Bam A Jos.


Hoto daga tashar Talabijin ta Najeriya na gungun jama'a da suka hallara kusa da gawarwakin wsu da aka kashe a rikicin Jos

Ana sauran makonni kafin a gudanar da zabe a Nigeria, jami’ai suka ce sun gano wani katon akwatin dake dauke da na’urar kera bam a birnin Jos jihar Plato.

Ana saura makonni kafin a gudanar da zabe a Nigeria, jami’ai suka ce sun gano wani katon akwatin dake dauke da na’urar kera bam a birnin Jos jihar Plato.

Jami’an soja sunce a ranar talata sojojin wata runduna ta musamman suka kama mutane biyu wadanda ke dauke da karikitan kera bam cikin wata jakar leda. Bayan da aka yiwa wadannan tambayoyin ne suka kai jami’an soja wani gida idan suka gano karin kayayyaki, ciki harda nakiya da wasu karikitan da kuma bayanin yadda za’a kera bam.

Haka kuma jami’an soja sun kama wani mutum na uku. Janaral Umaru Hassan ya fadawa kamfanin dilancin labarun Associated Press cewa mutane ne da suke son su hadasa rudami a lokacin zaben da za’a yi ne suke tara makamai.

XS
SM
MD
LG