Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An fara babban zabe na kasa a Najeriya


Voters queue to register during parliamentary elections in Kano, northern Nigeria.

Yau ake gudanar da zaben sabuwar majalisar tarayya a Najeriya

Yau ake gudanar da zaben sabuwar majalisar tarayya a Najeriya, wanda ya kasance zaben farko a jerin zabukan da za a dauki makonni uku ana gudanarwa. Masu sa ido suna jira su ga ko jami’an zabe zasu iya hana aukuwar tashin hankali da kuma kazamin magudin da aka tafka a zabukan da aka gudanar cikin shekara ta dubu biyu da bakwai, wanda masu sa ido na Kungiyar Tarayyar Turai suka bayyana a matsayin marar inganci, aka kuma dauki watanni ana kalubalantar zaben a kotuna. Shugaban hukumar zabe Attahiru Jega ya bayyana jiya jumma’a cewa, zaben da za a gudanar a wannan watan na Afrilu, wata dama ce da ‘yan Najeriya suke da ita na gyara kura-kuran da aka yi a lokutan baya. Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya bayyana gamsuwa da ci gaban da aka samu a Najeriya, ya kuma yi fatar zaben zai zama karbabbe ga ‘yan Najeriya da kuma al’ummar kasa da kasa. An yi fama da tashe tashen hankali a Najeriya yayinda ake shirin gudanar da zabukan musamman a arewacin kasar. Babu tabbacin ko dukan tashe tashen hankalun suna da nasaba da siyasa. An rufe kan iyakokin kasar da tafi kowacce yawan al’umma a Afrika daga karfe sha biyun rana jiya jumma’a zuwa shida na safiyar Lahadi. Hukumomi zasu kuma kayyade shawagin ababan hawa yayinda jama’a suke kada kuri’a.

XS
SM
MD
LG