Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wani Basarake Mai Dillancin Wiwi, Miyagun Kwayoyi A Sokoto


Wiwi 
Wiwi 

Duk da fafatuka da mahukunta ke yi akan hana sha da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya, har yanzu dai wannan matsalar na karuwa domin ana ci gaba da samun manyan mutane da hannu cikin wannan muguwar hada-hadar.

SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da hukumar da ke yaki da hada-hadar miyagun kwayoyi suka damke wani basarake wanda ke dillancin wiwi da kwayoyi a Jihar Sokoto, abin da ya sa masana ke ganin wata ishara ce ga mahukuntan kasar.

Batun sha ko hada-hadar miyagun kwayoyi ya jima yana ci wa 'yan Najeriya tuwo a kwarya duk da kokarin da mahukuntan ke yi na dakile matsalolin wanda ke da mummunar illa a cikin al'umma, musamman ga matasa.

Wannan karon wani basarake, jami'in da ke yaki da sha da safarar miyagun kwayoyin suka kama a Sokoto da hannu dumu-dumu ga dillancin kayan na maye.

Kwamandan hukumar a jihar, Adamu Muhammad Iro, ya ce sun share wata hudu suna kokarin kama basaraken amma sai yanzu ne suka samu nasara, dubunsa ta cika.

Wannan batun yana zuwa ne lokacin da 'yan kasa ke ci gaba da tsokaci tare da nuna yatsa ga hukuma akan yawaitar wadannan matsalolin a kasar.

Miyagun Kwayoyi
Miyagun Kwayoyi

Masana halayyar dan Adam na ganin wannan ba abin mamaki ba ne a samu shugaban jama'a da hannu ga aikata ba daidai ba, sai dai ya kamata ya kasance ishara wajen samar da shugabanni nan gaba, a cewar Farfesa Tukur Muhammad Baba.

Haka kuma jama'a na ganin su ma wadanda ke fafatukar dakile wannan safarar ya kamata a kara yawansu tare da karfafa musu gwiwa da samar da kayan aiki, kuma su kasance masu gaskiya, ta yadda za su iya kakkabe wannan muguwar safara a cikin al'umma.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

An Kama Wani Basarake Mai Dillancin Wiwi Da Miyagun Kwayoyi A Jihar Sakkwato.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

XS
SM
MD
LG