Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wani Likita Dan Najeriya Mazaunin Amurka Bayan Ya Mari Marar Lafiya


Onyekachi Nwabuko
Onyekachi Nwabuko

Jami’an ‘yan sanda a jihar Florida da ke Amurka sun kama wani likitan jinyar gaggawa dan Najeriya mazaunin Amurka, mai suna Onyekachi Nwabuko dan shekaru 44 da haihuwa, sabili da cin zarafin marar lafiya.

Bisa ga rahoton 'yan sandan, ya mammari wata mara lafiya da ba ta cikin hayyacinta saboda ya yi imanin cewa karyar sumewa ta ke ta yi.

Ma’aikatan jinya biyu, daraktan asibiti, da wanda abin ya shafa duk sun bayar da bayanan da suka kai ga kama Nwabuko. 'Yan sanda sun ce wadda aka mara din ta kuma samu "mummunan rauni a fuska."

Jami'an Sashen 'yan sanda na Leesburg da misalin karfe 8:00 na safe ranar 16 ga Fabrairu sun amsa kiran lambar gaggawa ta 911 game da lamarin da ya auku a Asibitin Kiwon Lafiya na Jami'ar Florida.

Bayan isa wurin, wasu ma’aikatan asibitin sun tabbatar wa ‘yan sanda cewa Nwabuko ya mari wadda ake jinyar sau da yawa a fuska domin ya yi imanin cewar suman da ta yi ba na gaske ba ne.

Nwabuko ya yi amfani da hannun matar da ake jinya, ya mare ta da shi a fuskarta.

"Ki yi min afuwa, dole ne in yi hakan," Nwabuko ya fada yayin da yake marin ta da hannun ta.

Wacce abin ya shafa ta shaida wa ‘yan sanda cewa “tana cikin hayacinta rabi-da-rabi” amma ta tuna da lokacin da Nwabuko ya mare ta kuma ya ke fadi mata cewa “karya ta ke yi.”

Ya ci gaba da marin ta har sai da ma’aikatan jinya suka sa baki a cikin lamarin,” a cewar ta.

An kai Nwabuko zuwa gidan yarin Lake County da ke Tavares a jihar Florida bayan faruwar lamarin.

Yanzu haka an sake shi bayan ya biya da kudin beli dala 3,000 (kimanin Naira miliyan 1.7).

Za a dai gurfanar da shi a ranar 3 ga Maris 2022.

XS
SM
MD
LG