Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wani Limamin Krista Da Laifin Yiwa Gwamnatin Zimbabwe Zagon Kasa


Pastor Evan Mawarire

‘Yan sandan kasar Zimbabwe sun kama wani dan gwaggwarmaya kuma Pastor Evan Mawarire saboda ya aika da wani sako ta hanyar sada zumunci yana kira ga al’ummar kasar su gudanar da zanga zanga kan karancin mai da kuma Karin farashin kayan masarufi da aka yi.

‘Yan sanda sun jira Mawarire a bakin kofar majami’a lokacin da yake jagorancin sujadar safe.

Lauyan Harrison Nkomo na kungiyar lauyoyin kasar Zimbwe dake kare hakkin bil’ama shine ke wakiltar limanin, wanda kuma shine shugaban gangamin nan da dake #thisflag wadda bara ta jagoranci zanga zanga da dama a aka yiwa gwamnati.

An kama Evan ana zarginshi da yiwa gwamnatin da aka zaba zagon kasa. A bayyane yake bisa ga hoton bidiyon da aka yayata jiya dangane da layuka a gidan mai da kuma tashin gwauron zabo na farashin kayan masarufi a shaguna.”

Gobe ake kyautata zaton gurfanar da Pastor Mawarire a kotu, jiya asabar gwamnatin Amurka ta fitar da sanarwa tana kira ga Harare ta bari a yiwa Mawarire shari’ar adalci, wanda yake fuskantar wata tuhuma ta daban da ake zarginsa da kokarin yiwa gwamnatin shugaba Robert Mugabe zagon kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG