Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu ‘Yan Bindiga Da Wani Hakimi Kan Zargin Yin Garkuwa da Mutane a Jihar Neja


Yan Sandan Najeriya

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wasu mutane goma sha biyu, a ciki har da hakimin Gurmana, Alhaji Aliyu Umar bisa zarginsu da zama muggan masu garkuwa da mutane da kuma satar shanu a jihar Neja.

‘Yan sandan sun kama basaraken ne da sauran mutanen a cikin wata musayar wutar da tayi sanadiyar raunata wani dan sanda guda. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Mr. D.P. Yakadi yace sun samu makamai da dama, ciki har da bindiga kirar AK47 a hannun mutanen.

Kwamishinan ‘yan sandan Nejan yace sun dade suna fama da ta’addanci a yankin Alawa da Kagara da sauran wurare a cikin jihar. Yace yanzu ne suka samu nasarar kama wadannan mutane kuma suna gudanar da bincike a kansu.

Kungiyar Miyeti Allah ta yi marhaba da kama wadannan mutane kuma tayi kira da a tabbatar da gaskiya kamar yanda shugaban kungiyar na kasa Alhaji Husseini Boso ya fadawa wakilinmu Mustapha Nasiru Batsari a birnin Minna.

Wasu mutanen yankin Gurmana dake cikin wani yanayi na rudani a kan wannan al’amari, sun nemi a sakaya sunayensu yayinda suke zantawa da Muryar Amurka.

Ga dai Rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Minna:

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG