Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Wasu Sojojin Najeriya A Mali Zasu Koma Gida


Sojojin Najeriya dake shirin zuwa Mali tun farko daga Kaduna.

Domin su taimaka a yakin da kasar ke yi da tsageran kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnati Lidda'awati Wal Jihad, wadda aka fi sani da sunan Boko Haram

Yau laraba wata bataliya guda ta sojojin Najeriya dake taimakawa wajen yakar 'yan kishin Islama a kasar Mali, zata koma gida domin gudanar da irin wannan aiki a yakin da kasar keyi da 'yan Boko Haram.

Kakakin ma'aikatar tsaron Najeriya, Birgediya-Janar Chris Olukolade, ya fada jiya talata cewa da komowarsu za a tura wasu daga cikin wadannan sojoji bakin daga.

Bataliya guda dai tana kumsar sojoji kimanin 700. Najeriya ta tura sojoji har dubu daya da dari biyu zuwa Mali domin taimakawa kasar wajen fatattakar 'yan kishin Islama da suka mamaye arewacinta.

Birgediya Olukolade yace Najeriya zata ci gaba da tallafawa yunkurin da ake yi a kasar ta Mali ta wasu hanyoyin, ciki har da "samar da cikakken asibitin soja, da wasu sojoji na sigina da hafsoshin da zasu gudanar da ayyuka a hedkwatar rundunar dake Mali.

A baya cikin watan nan na Yuli, Kungiyar Kasashen Afirka ta ce Najeriya zata janye wasu daga cikin sojojinta dake Mali domin su sanya hannu a yakin da ake yi da 'yan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Wasu daga ckin sojojin dake yakar 'yan bindigar na Boko Haram yanzu haka, musamman a jihohin Borno da Yobe, sun yi kuka ga kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa an fi shekara biyu da tura su bakin dagar, dubban kilomitoci daga iyalai da 'yan'uwansu.
XS
SM
MD
LG