Yayin da matsalar fyade ke kara karuwa fiye da wutar daji a Najeriya, rundunar tsaron farin kaya ta Sibil Difens a jihar Adamawa, na samun nasara wajen bankado mabuyar wadannan bata gari dake addabar al’umma.
A kwanakin baya ne aka cafke wani jagoran wasu da kewa kananan yara fyade a Yola, inda dubunsa ta cika. Nuraddeen Abdullahi kwamandan rundunar tsaron ta sibil difens a jihar, yace wanda aka kama mai kimanin shekaru 30 da haihuwa, Mohammad Babangida an cafke shi ne yana yiwa wata 'yar shekara tara fyade.
A wata sabuwa kuma jami’an 'yan sanda a jihar, sun kai samame wani gidan tsare kangararru, inda ake tsare jama’a ba bisa ka’ida ba. A lokacin wannan samame an kubutar da mutane 15.
DSP Suleiman Yahya Nguroje, wanda shine kakakin rundunar 'yan sandan jihar yayi wa wakilin muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz karin haske game da wannan batu.
Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 29, 2023
CBN Ya Kara Kwana 10 Kan Wa’adin Daina Karbar Tsofaffin Kudi
-
Janairu 27, 2023
Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Kauce Hanya
-
Janairu 27, 2023
Za Mu Daukaka Kara – Adeleke
Facebook Forum