Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Gano Wasu Masu Cutar Coronavirus A Legas


Hukumomin lafiya a jihar Legas sun tabbatar da samun karin mutum hudu masu dauke da cutar coronavirus a Najeriya, yanzu adadin wadanda cutar ta kama ya kai mutum 12.

A yau Alhamis 19 ga watan Maris, kwamishinan lafiya na jihar Legas Akin Abayomi ya yi wa manema labarai jawabi game da karin masu cutar da aka samu a sakatariyar jihar. Ya kuma bayyana cewa an killace mutanen a asibitin dake unguwar Yaba a birnin Legas.

Mr. Abayomi ya ce a jiya Laraba ne aka gwada mutane goma sha tara wadanda aka kyautata zaton sun kamu da cutar kuma sakamakon gwajin ya tabbatar da cewa hudu daga cikin su suna da cutar.

Hakazalika hukumomi na neman wasu mutane kimanin 130, ciki har da fasinjojin jiragen saman da marasa lafiyan suka shiga.

Saurari karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG