Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Dakile Cututtuka Ta Afrika Ta Ce Dole Nahiyar Ta Tashi Tsaye


Kasashen Afrika uku ne cutar coronavirus ta fi kamari a daukacin nahiyar, amma mataimakin daraktan hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika da ake kira ACDC, ya ce ya zama wajibi nahiyar ta yi nata kokarin wajen daukar matakan kariya.

“Kwayar cutar na haddasa matsaloli a sauran sassan duniya, don haka mu a Afrika dole mu kasance a cikin shiri, kada ta yi mana irin kaka-gidan da ta yi wa kasashen Turai da Asiya. Domin kuwa tsarin kiwon lafiyar mu ba zai iya tunkararta ba.” Abinda Dr. Ahmed Ogwell ya fadawa Muryar Amurka kenan.

Ogwell ya kara da cewa hukumarsa ta ACDC, wadda ke karkashin kungiyar hadin kan kasashen Afrika, na kokarin karfafa matakan kariyar kasashe ta hanyoyi uku, ciki har da inganta matakan sa ido a iyakokin kasashe da kuma asibitoci; kara wa kasashe damar yin gwaje-gwajen cutar ta COVID-19, wanda yanzu kasashen Afrika 43 ne kawai ke da wadannan kayayyakin gwajin; da kuma karfafa matakan dakile yaduwar cututtuka da magance su ta yadda za a killace marasa lafiya a kuma sa ido akansu.

Ya zuwa yau, kasashen da cutar ta fi shafa sun hada da Masar mai mutane 196 da suka kamu da cutar, da Afrika ta Kudu dake da mutane 116, sai kuma kasar Algeria da aka sami mutane 73 dake dauke da cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG