Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe akalla mutane talatin a bata kashi da aka yi a Libya


A wounded man is carried into the al-Jala hospital in Benghazi after an attack by Libyan military forces loyal to Muammar Gaddafi on a weapons dump near Benghazi in rebel-controlled eastern Libya killed 17 people.

An bada rahoton cewa an kashe akalla mutane talatin ciki harda wani shugaban yan tawaye a mumunar bata kashin da aka yi a yayinda sojojin dake biyaya ga shugaba Moammar Gaddafi na Libya suka kaddamar da wani sumame a jiya juma’a domin sake kwace garin AZZawiyah dake hannun ‘yan tawaye.

An bada rahoton cewa an kashe akalla mutane talatin ciki harda wani shugaban yan tawaye a mumunar bata kashin da aka yi a yayinda sojojin dake biyaya ga shugaba Moammar Gaddafi na Libya suka kaddamar da wani sumame a jiya juma’a domin sake kwace garin AZZawiyah dake hannun ‘yan tawaye an bada rahoton cewa an kashe akalla mutane talatin ciki harda wani shugaban yan tawaye a mumunar bata kashin da aka yi a yayinda sojojin dake biyaya ga shugaba Moammar Gaddafi na Libya suka kaddamar da wani sumame a jiya juma’a domin sake kwace garin AZZawiyah dake hannun ‘yan tawaye. Kafofin yada labaru sun ambaci shedun gani da ido na fadin cewa mutanen sun mutu ne a arangamomin da aka yi a ciki da kewayen garin Zawiyah, kimamin kilomita hamsin yamma da birnin Tripoli. A yanzu haka dai ba’a dai tance tance ko wane bangare ne ke iko da garin. A halin da ake ciki kuma, rahotani na fadin cewa akalla mutane goma sha bakwai ne suka mutu a sakamakon tashin wani bam daya girgiza birnin Benghazi a jiya juma’a da dare. Kamfanin dilancin labarun Reuters ya ambaci wani shugaban masu hamaiya yana fadin cewa sojojin Gaddafi ne suka kaiwa wani wurin adana makamai a wajen birnin hari. Haka kuma sojojin dake biyaya ga Mr Gaddafi sunyi amfani da barkonin tsohuwa akan masu zanga zanmgar a birnin Tripoli. Daruruwan mutane ne suka yi zanga zangar kin jinin gwamnati bayan sallar Juma’a, harma wasu suka yi ta kururuta cewa Gaddafi baya kaunar Allah. An kuma bada rahoto cewa an ci gaba da tapka fada tsakanin bangarorin biyu a birnin Ras Lanuf mai tashar jiragen ruwa. Tunda farko a jiya juma’a jiragen saman yakin Libya sun kai hare haren da suka auna wani sansanin soja kusa da garin Ajdabiya dake hannun yan tawaye a gabashin kasar

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG