Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Bayan Gadhafi Sun Cika Titunan Birnin Tripoli


Pro-Gadhafi soldiers and supporters gather to celebrate in Green Square, Tripoli, Libya.

Magoya bayan shugaban Libya Moammar Gadhafi sun cika titunan birnin Tripoli, ran lahadi suna murna da shewa bayan samun nasarar da sojin Gwamnati suka yi wajen sake kwato wasu muhimman biranen kasar Libya. Amma mazauna biranen sun musanta wannan ikrari na sake kwato biranen daga hannun ‘yan tawaye.

Gidan Telbijin na Libya ya bada rahoton cewa sojin dake biyayya ga shugaba Gadhafi sun sake kame birnin Misrata daga hannun mayakan ‘yan tawayen Libya. Kazalika Gwamnatin Libya tace sojinta sun sake kwato muhimmin garin nan Ras Lanuf, mai albarkatun man fetur dake gabar teku. Magoya bayan shugaba Gadhafi saidaga tutocin Libya suka rika yi a kan tituna, suna busa kahonni da matsa hon na mota wasu harda harba bindiga sama a birnin Tripoli domin murnan wannan nasarar ta sake kwato biranen da sojin Gwamnati suka yi daga hannun ‘yan tawayen Libya. Mayakan ‘yan tawayen Libya sun kakkame wurare masu muhimmancin gaske a yankin gabashi, kuma ‘yan tawayen sun lashi takobin sai sun kama Tripoli, babban birnin kasar wanda yanzu haka ke karkashin ikon Shugaba Gadhafi.

Pro-Gadhafi forces outside al-Zawiya, Libya

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG