Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yakin Libya Sun Kai Hare-Hare Kan Muhimman Tasoshin Mai


Wani bam din da jiragen yakin Libiya suka jeho kenan ya tarwatse a Brega.

Shaidun gani da ido sun ce jiragen yakin Libya sun kai wasu sabbin hare hare a yau Alhamis akan tashar man Brega da ke gabashin kasar, kwana guda da dakarun ‘yan tawaye su ka fattaki sojojin da ke biyayya ga Shugaba Moummar Gaddafi daga birnin.

Shaidun gani da ido sun ce jiragen yakin Libya sun kai wasu sabbin hare hare a yau Alhamis akan tashar man Brega da ke gabashin kasar, kwana guda da dakarun ‘yan tawaye su ka fattaki sojojin da ke biyayya ga Shugaba Moummar Gaddafi daga birnin.

Dakarun ‘yan tawaye sun fatattaki sojojin da ke biyayya ga Gaddafi, da su ka kai masu gagarimin farmaki ta kasa da ta sama a jiya Laraba a karo na farko a gabashin kasar da ke karkashin ikon su ‘yan tawayen.

Shaidun gani da ido sun ce sojojin da ke biyayya ga Gaddafi da ke tafe da motocin yaki sama da hamsin sun sun dira birnin Brega, wanda ke kusa da kogin Sirte mai kuma nisan kilomita 800 daga, Tripoli, babban birnmin kasar. Ba tare da bata lokaci bas u ka kwace tashoshin man da ke birnin da tasoshin jiragen sama da ne ruwa.

Labarin harin ya sa mayakan sa kai sun danno daga garuruwan da ke kusa irinsu Ajdabiya da Benghazi, su ka tinkare su da bindigogin AK-47, da kuma rokoki da tsoffin tankokin yaki da sauran kayan fada.

Sojojin ‘yan tawayen sun mayar da martanin ne da yamma, inda su ka kori sojojin da ke goyon bayan Gaddafi daga birnin. Likitoci sun bayar da rahoton mutuwar akalla muatne 12 a wannan fadan. A lokacin fafatawar, jiragen yaki sanfurin jet-jet sun yi ta barin wuta kan dakarun ‘yan tawayen a birnin na Brega da kuma bayan garin Adjabiya, inda ake da dinbin makaman da ke karkashin ikon ‘yan tawaye.

An yi arangamar ta Brega ce a daidai lokacin da Majalisar Gwamnatin Wucin gadin ‘yan tawayen ke kiraye-kirayen kasashen waje su kai hari ta jiragen sama kan sosojin haya bakaken fatan da su ka ce Gaddafi na amafani da su wajen murkushe tawayen.

A halin da ake ciki kuma Sakatare-janar na Kungiyar Kawancen NATO ya fadi yau Alhamis cewa kungiayar bat a da niyya shiga cikin rikicin na Libya, to amman tana shirin ko ta kwana.

Anders Fogh Rasmussen y ace jama’an NATO na lura da yadda al’amura ke gudana sosai.

Wannan bayanin nasa ya zo ne rana guda bayan da kungiyar kasashen Larabawa ta ki amincewa da duk wani sa hannun sojojin kasashen waje kai tsaye kuma wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka ke kaffa-kaffa da wannan zabin.

Ministatocin kasashe 22 da ke kungiyar sun fadi jiya Laraba cewa sun a iya goyon bayan batun hana jirage gittawa wasu sassan Libya kuma za su yi duk abin das u ke iyawa don kare ‘yan Libya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG