Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Babban Jami’in Hamas A Wani Hari Da Isra’ila Ta Kai


Zirin Gaza
Zirin Gaza

Wani jirgin saman yakin Isra'ila mara matuki ya kai hari kan ofisoshin Hamas da ke yankin Beirut a daren jiya Talata, inda ya kashe babban jami'in Hamas Saleh al-Arouri, kamar yadda kungiyar mayakan da kafar yada labaran Mideast suka bayyana.

WASHINGTON, D. C. - Arouri babban jami'i ne a tsarin shugabancin kungiyar ta Hamas, kuma daya daga cikin wadanda suka kafa reshen soji na kungiyar dakarun Qassam Brigades, wadanda suka kai wani mummunan hari a yankin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

A bara Amurka ta yi tayin ladan kudi dala miliyan 5 ga wanda ya ba da bayanai game da shi.

Rundunar sojin Isra'ila ta ki cewa komai kan rahoton, amma irin wannan harin ya yi dai dai da kudurin da birnin na Kudus ya yi na kashe wasu manyan shugabannin Hamas, a yayin da yakin da Hamas a Gaza ya kusa cika watanni uku.

Arouri ya jagoranci kasancewar Hamas a yankin yammacin gabar kogin Urdun da Isra'ila ta mamaye. Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi barazanar kashe shi tun ma kafin kungiyar mayakan ta kai mamaya a kudancin Isra'ila a harin na watan Oktoba.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG