Accessibility links

An Kashe Dan Sanda Da Mai Talla A Bauci


Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Bauchi, Mohammed Ladan, yana bayani ga 'yan jarida game da tashin bam a harabar majami'ar Harvest Field Church dake Unguwar Yelwa a Bauchi, lahadi 3 Yuni 2012.

A jihar Bauci wassu yan bindiga sun kashe wani jami'in yan sanda mobile dakuma wata mace budurwa mai talla a daren jiya litinin a garin Darazo shalkwatar karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi.

Kwamishinan ‘Yan Sanda a jihar, Muhammed Ladan ya tabbatar da wannan labari. Yace barayi ne suka aikata wannan ta’asa.

Shugaban karamar hukumar Darazo Alhaji Kabir Tade yace komai ya lafa a halin yanzu. Yace: Yanzu dai koma ya lafa, ana ta wal-wala kurum. Sai dai munyi kokari, wadanda suka ji raunuka duk mun bada kudin magani da komai da komai.

Wani mazaunin garin da bai fadi sunanshi ya fada cewa: Yanzu dai komai ya lafa, amma mu dai bamu san wani hali ake ciki ba. Babu alaman hayaki, sai dai dan harbe-harbe da aka yi na sa’o’i uku.

XS
SM
MD
LG