Accessibility links

An Kashe Kwamandojin Boko Haram Biyu A Adamawa

  • Garba Suleiman

Wasu daga cikin sojojin da aka tura Adamawa domin yakar Boko Haram

Rundunar sojan Najeeriya ta ce an kashe Mohammed Bama da Abubakar Zakari Ya'u a musanyar wuta a garin Mubi

Sojojin Najeriya sun kashe wasu manyan kwamnadoji guda biyu na kungiyar Boko Haram a lokacin musanyar wuta na tsawon sa'o'i hudu a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya.

Kwamandan sojojin Najeriya dake garin Mubi a Jihar Adamawa, Beyidi Marcus Martins, ya fadawa 'yan jarida yau laraba cewa an kama Mohammad Bama da Abubakar Zakari Ya'u a kusa da garin Mubi a makon da ya shige, kuma sun furta cewa sun shirya kai hari a Jihar Taraba.

Wadannan kwamandojin biyu na Boko Haram sun dauki jami'an soja domin nuna musu maboyarsu a garin Mubi, amma sai aka goce da musanyar wuta a garin in ji jami;'in sojan. Yace an kashe wasu 'ya;yan kungiyar ta Boko Haram a wannan maboya.

Gwamnatin Najeriya dai ta saka tukuicin Naira miliyan 10 ga duk wanda ya kamo ko ya kashe Mohammad Bama ko Abubakar Zakari Ya'u.

Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da yadda aka yi kwamandojin biyu na Boko haram suka mutu, haka kuma ita ma kungiyar ta Boko Haram ba ta ce uffan ba game da hasarar kwamandojinta.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun zargi sojojin Najeriya da laifin kashe mutanen da suka kama da rai ba tare da an gurfanar da su gaban shari'a ba, a yakin da suke yi da Boko Haram. Rundunar sojan Najeriya dai ta sha musanta wannan zargin.
XS
SM
MD
LG