Accessibility links

Mutane 59 Ne Suka Mutu A Hare-Haren Karshen Mako A Borno


'Yan Najeriya dake arewa maso gashin kasar, mahaifar kungiyar Islama mai tsatsauran ra'ayi sun yi bikin karamar sallah ranar Alhamis da addu'o'i cikin murna da annashuwa da gaisuwar bangirma da jama'a fiye da 10,000 suka kaiwa Shehun Borno a fadarsa.

Hakimin Konduga, yace akwai mata cikin ‘yan bindigar da suka kai hari a garin ranar lahadi, yayin da gwamna Kashim shettima ya kai ziyarar gani da ido jiya talata

Hukumomin Jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin Najeriya sun ce a yanzu mutane akalla 59 ne aka tabbatar sun mutyu a hare-haren da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wasu garuruwa biyu dake kusa da Maiduguri, babban birnin Jihar.

A hari guda, wasu ‘yan bindigar da suka yi shiga irinta sojoji, sun kai farmaki a kan garin Konduga ranar lahadi da asuba, suka bude wuta kan mutanen dake yin sallar asuba a cikin wani masallaci. Haka kuma, sun cunna wuta a gidajen dake kusa da nan. ‘Yan sanda suka ce an kasha mutane 47, aka ji rauni ma wasu 39. Sannan an kona gidaje guda hamsin.

Hakimin Konduga, Zannah Musa Yale, yace wasu daga cikin wadannan mahara mata ne. Gwamna Shettima Kashim na Jihar Borno ya ziyarci garin na Konduga jiya talatya ya kuma yi alkawarin biyan diyya ga iyalan da abin ya shafa.

A wani harin dabam, ‘yan bindigar sun shiga kauyen Ngom suka kasha mutane 12 daren asabar.

Babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai wannan harin, amma jami’ai sun a kyautata zaton kungiyar nan ce ta Boko Haram ta kai. A baya, kungiuyar Boko Haram ta dauki alhakin kai hare-haren da suka hada har da kan masallatan da limamansu suka yi tur da tsagerancin addini.
XS
SM
MD
LG