Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Masu Ibada Tara a Cocin Pakistan


Motocin sojoji da aka girke a wajen cocin da aka kai hari a Pakistan ranar 17, ga watan Disambar 2017.
Motocin sojoji da aka girke a wajen cocin da aka kai hari a Pakistan ranar 17, ga watan Disambar 2017.

Wasu 'Yan Kunar Bakin Wake sun kai hari a wata mujami'a da ke Pakistan, inda suka kashe akalla mutum tara.

Akalla wasu ‘yan kunar harin bakin wake biyu ne dauke da manyan makamai suka kai hari wata mujami’a da ke Quetta a kudu maso yammacin Pakistan.

Sun kashe Kiristoci masu ibada akalla tara, wadanda tsiraru ne a kasar ta Pakistan.

Jami’an kasar sun ce akwai yara kanana da mata a cikin wadanda harin ya rutsa da su wanda aka kai kan mujami’ar Bethel Memorial Methodist da ke wani yankin tsakiyar garin mai cike da tsaro.

Wadanda suka shaida harin sun ce, maharan sun yi yunkurin shiga cikin babban dakin cocin mai dauke da mutum kusan 400.

Amma ‘yan sanda suka dakile su suka fara musayar wuta da su, har suka kashe daya daga cikinsu, yayin da dayan kuma ya tarwatsa kansa da bam ya ji wa wani jami’in tsaro mummunan rauni.

Shugaban ‘yan sandan Lardin, Janar Moazzam Ansari, ya ce, wani mahari na uku ya tsere yayin musayar wutar, amma ana kan farautarsa.

Ansari ya kara da cewa daba don an dakile shigar maharan cikin cocin ba da adadin mutanen da suka mutu ya haura haka.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG